Ganduje ya bada umarnin bude Filin Wasa na Sani Abacha gabanin ziyarar Atiku

182
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin a dakatar da kwaskwarimar da ake yi wa Filin Wasa na Sani Abacha don ba dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar damar gudanar da yakin neman zabensa.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan Wata Labarai na jihar, Muhammad Garba.

A ranar Talata ne rahotanni suka bazo cewa Gwamnatin Jihar ta bada umarnin rufe dukkan filayen wasan jihar, wani abu da ake ganin na da dangantaka da yakin neman zaben da Atiku zai gudanar a jihar Kano ranar 10 ga watan Fabrairu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan