Kakar yakin neman zabe: Buhari zai je Legas ranar Asabar

155

Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa dan takararta na shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kasance a jihar Legas ranar Asabar don gudanar da yakin neman zabe.

Jihar Legas ce jiha ce da jam’iyyar APCn ke alfahari da ita sakamakon dimbin magoya baya da take da su a jihar.

Duk da za a gudanar da yakin neman zaben ne a karshen mako, ana sa ran zai kawo cunkoson ababen hawa.

Kafin gagarumin yakin neman zaben, Shugaba Buhari zai ziyarci wasu wurare da suka hada da fadar Oba na Legas, Rilwan Akiolu.

A ranar Talata ne Shugaban ya je jihar Ekiti inda ya gana da shugabannin gargajiya ya kuma nemi goyon bayansu don samun nasara a zabe mai zuwa.

A yayin yakin neman zaben na Ekiti, Shugaban ya ce bai saba wa ‘yan Najeriya alkawarin da ya yi musu ba shekara ta 2015, inda ya yi alkawarin inganta tsaro, yaki da cin hanci da tayar da fadada tattalin arziki.

Ya gode wa a’lumar jihar ta Ekiti bisa zaben gwamna da suka yi ranar 14 ga watan Yuli, 2018 wanda jam’iyyar APCn ta lashe.

Da suke mayar da jawabi, Oba Joseph Adewole, Ajero na Ijeru Ekiti kuma Sakataren Majalisar Sarakunan Jihar, ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya nada minista daga jihar don maye gurbin Gwamna Fayemi a majalisar ministocinsa.

Sun kuma yi kira gare shi da ya gyara hanyoyin Gwamnatin Tarayya dake jihar sakamakon lalacewa da suka yi.

Daga sun bukace shi da ya kawo karshen yajin aikin ASUU don dalibai su samu su koma makaranta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan