Zabe: Sirleaf ta gana da Shugaban INEC

167
Shugabar Shirin Sa Ido na ECOWAS, Ellen Johnson Sirleaf ta gana da Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu a hedikwatar Hukumar Zaben Mai Zaman Kanta ta Kasa dake Abuja

A ranar Laraba ne Shugabar Shirin Sa Ido na ECOWAS, Ellen Johnson Sirleaf ta gana da Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu a hedikwatar Hukumar Zaben Mai Zaman Kanta ta Kasa dake Abuja[/caption] Sa Ido na Kasashen ECOWAS kuma tsohuwar Shugabar Laberiya, Ellen Johnson Sirleaf, ta gana da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu a hedikwatar Hukumar dake Abuja, inda ta yi alkawarin tabbatar da zabe cikin lumana da adalci a Najeriya.

Misis Sirleaf, wadda ta iso Najeriya ranar Talata ta ce dalilin ziyararta shi ne ta samu bayanai game da zabukan Najeriya.

Mataimakiyar Shugaban Hukumar ECOWAS, Misis Fanda ce ta karbe ta a Sashin Saukar Jirgin Shugaban
Kasa dake Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Nnamdi Azikwe dake Abuja ranar Talata.

Ta kuma samu tarbar sauran mambobin Hukumar da kuma wakilan Majalisar Dokoki ta ECOWAS.

“Ina fatan haduwa da shugabannin siyasa, ina son in fahimci rawar da zan taka don tabbatar da cewa na shirya tsaf don gudanar da aikin.

“Na ji dadi da ya zama aiki ne na ECOWAS, zan rika yin aiki da su (Hukumar ECOWAS) kuma za su yi min jagora, kuma ina fatan zan bi sahun ‘yan Najeriya don tabbatar da cewa gaba dayan wannan zaben an yi shi cikin lumana da nasara.

“Wannan shi ne makasudin aikina”, in ji Misis Sirleaf.

“Ba zan iya cewa komai ba har sai na samu damar isar da sakamakon aikin baya, na samu tuntubar wadanda suke a kasa.

“A dan lokaci kadan mai zuwa, Shirin Sa Ido na ECOWAS zai ta yin aiki tukuru, zai gudanar da aikinsa zai kuma yi jawabi idan lokacin jawabi ya yi”, a kalaman Misis Sirleaf.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan