Abinda ya kamata ku sani game da sabon Kwamishinan ƴan Sandana Kano

150
Sabon Kwamishinan 'Yan Sanda na jihar Kano, Mohammed Wakili

An turo Mohammed Wakili, dan sandan nan da ya bayyana a wani faifan bidiyo yana magana game da yawan shan kwayoyi zuwa jihar Kano a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda.

Mista Wakili ya gaji Rabi’u Yusuf ne, wanda har yanzu bai samu sabon mukami ba.

Daily Nigerian ta gano cewa Mista Wakili, wanda daya ne daga cikin jami’ai masu binciko bayanan sirri a Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, yana da wata uku ne kawai kafin ya yi ritaya.

Yadda Mista Wakili ya bayyana a wani faifan bidiyo yana magana game da shan muggan kwayoyi kamar a fim ya ba mutane ma’abota amfani da Intanet dariya sosai.

“Shan kwaya ya zama ruwan dare a cikin al’uma.

“Ko ina kwaya, kowa yana kuka game da shan kwaya, maza kwaya, mata kwaya, manya kwaya, yara kwaya”, in ji Mista Wakili.

Rahotanni dai na cewa jihar Kano ce akan gaba wajen shan kwaya.

Ko a ranar Litinin da ta gabata, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA ta ce ta tarwatsa wuraren siyar da kwaya har guda 35 a jihar Kano.

Kwamandan Hukumar a jihar, Ibrahim Abdul ya ce an samu wannan nasarar ne sakamakon jajircewar ma’aikatan Hukuma lokacin da aka ba su horo na musamman don raba jihar da shan kwaya yayinda zaben 2019 ke kuratowa.

“A lokacin wannan aiki, an tarwatsa wuraren siyar da kwaya har guda 35 kamar haka: Plaza, Sanya Olu, Kabuga, Rimin Kebe da Danzaki.

“Sauran su ne Sauna, Wurare, Aisami, Sabon Titi, Dorayi, Hauren Gadagi, tashar Kwanar Danmarke Chalawa, Madobi, Ring Road, Farawa, tashar Mariri, Kofar Ruwa da sauransu”, in ji Mista Abdul.

Majiyoyin cikin gida sun ce sabon Kwamishinan yana da dama da karfin gwiwar da zai yaki mummunar dabi’ar shan muggan kwayoyi a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan