Shirye-shiryen zaɓe: INEC ta fara ba ma’aikata 850,000 horo

155

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce ta fara ba ma’aikata 850,000 da suka hada da ma’aikacin wucin gadi horo don gudanar da zabukan 2019.

Bangaren farko na na bada horon wanda aka fara a Kalaba ranar Litinin ya hada da Jami’an Bada Horo na Jiha da Mataimaka Jami’an Bada Horo daga jihohi 36 na kasar nan, wadanda su ma za su ba wasu jami’an horo a matakai daban-daban.

Shugaban Cibiyar Zabe ta INEC wadda ke da alhakin bada horon a INEC, Mista Solomon Soyebi ne ya bude bada horon a madadin Shugaban Hukumar Zaben, Farfesa Mahmud Yakubu.

“Wannan wani yunkuri ne na Hukumar Zaben don tabbatar da cewa mun shirya tsaf don zabukan shekara ta 2019”, a cewar Mista Soyebi lokacin da yake bude bada horon.

Ya ce a kalla ma’aikata miliyan daya ne za su yi aikin zaben, kuma dukkanninsu za su karbi horo daga wannan mako zuwa mako mai kamawa.
Ya ce: “Hukumar ta lashi takobin gudanar da zabe na fili, na adalci kuma karbabbe ko duk wahalar haka ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019”.

Mista Soyebi ya kuma yi magana game da yadda mutane masu bukata ta musamman za su kada kuri’a a dukkan zabukan, yana mai cewa: “Ba wata dimokuradiyyar da za ta zama cikakkiya ba tare da lura da mutane masu bukata ta musamman ba”.
Ya gode wa Gidauniyar Kula da Tsare-tsaren Zabe ta Kasa da Kasa, IFES, sakamakon tallafa wa shirin bada horon da kudi da kuma ma’aikata.

Mukaddashin Darakta Janar na Cibiyar Zaben, Dakta Idris Umar ya fada wa masu karbar horon cewa: “Ba za mu iya gudanar da zabuka na fili kuma na adalci ba ba tare da ma’aikata da suka samu isasshen horo ba. Sama da mutane 850,000 za a ba horo don gudanar da manyan zabukan, kuma nauyi ya rataya a wuyanku wajen gabatar da kyakkyawan horo a dukkan matakai”.

Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar, Dakta Frankland Briyayi ya ce bayan horon na kwana wadanda suka karbi horon za su koma jihohinsu daban-daban don aiwatar da abinda suka koya.

Daraktan IFES, mai kula da bada horon, Seray Jay ya ce aikin da yake akan masu karbar horon yana da yawa, ya hore su da su dauki bada horon da muhimmancin gaske.

Shugaban Gidauniyar Zabaya, Jake Epelle ya ce ba wa kowa dama shi ne abinda yake sa zabe ya zama karbabbe, ya kuma gode wa INEC bisa saka mutane masu bukata ta musamman da ta yi a tsare-tsaren zabenta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan