Cikin Kankanin Lokaci Zan Kammala Aikin Samar Da Hasken Lantarki Na Mambilla – Atiku

184

Ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin kammala ginin tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla, idan har ‘yan Nigeria suka zabe shi a matsayin shugaban kasa

Atiku ya sha wannan alwashin ne a garin Jalingo, jihar Taraba, a lokacin da ya ke kaddamar da yakin zabensa.

Ya ce gwamnati mai ci a yanzu na yiwa aikin tafiyar hawainiya, tare da gazawa wajen biyan hakkokin jama’a da aka karbi filayensu, uwa uba kuma gaza kai ‘yan kwangila a wurin aikin, inda ya sha alwashin mayar da hankali wajen gina manyan titunan gwamnatin tarayya na jihar.

Atiku ya lashi takobin kammala ginin cibiyar samar da lantarki ta Mambilla. Ya jaddada bukatar da ke da akwai na jami’an tsaro da su kasance marasa nuna banbanci a lokacin gudanar da ayyukansu, musamman ma a lokacin gudanar da babban zabe na 2019.

A Karshe Atiku ya bukaci masu kad’a kuri’a a Taraba da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabarsa a ranar 16 ga watan Fabreru, inda ya sha alwashin samar da ayyukan raya kasa a gare su.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan