INEC ta kara lokacin karbar Katinan Zabe

38
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu

A ranar Juma’a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta sanar da cewa ta kara lokacin karɓar Katinan Zabe na Din-din-din har zuwa Litinin.

INEC ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter, tana mai bayyana cewa karbar Katinan Zaben da da aka shirya rufewa ranar Juma’a (yau) a yanzu zai kai zuwa karshen mako (Asabar da Lahadi) zuwa Litinin lokacin da za a rufe karbar Katinan Zaben a dukkan fadin kasa.

“Karbar Katinan Zabe na Din-din-din, PVCs da da aka shirya rufewa yau Juma’a, 8 ga watan Fabrairu, 2019, a yanzu an kara shi a dukkan fadin kasar nan zuwa Litinin, 11 ga watan Fabrairu, 2019. Wannan zai hada da Asabar da Lahadi.

“A yanzu za a rika fara karbar Katinan Zaben daga karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma kullum. Ana umartar dukkanin ofishin jihohi da su yi bitar tsarin karbar Katinan Zaben na Din-din-din, su kuma sa dukkan ma’aikatan ofisoshin kananan hukumomi a aikin karbar Katinan Zaben”, a cewar sanarwar.

Sanarwar ta shawarci ma’aikatan Hukumar Zaben da su zama masu kyawawar mu’amala ga ‘yan kasa da za su zo karbar Katinan Zaben, su kuma kai rahoton duk wasu abubuwa da ba za su iya warwarewa ba zuwa ga na gaba da su.

“Hukumar Zaben tana son tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba wani dan Najeriya da yake da rijista da za a hana shi damarsa ta kada kuri’a bisa rashin karbar Katin Zabe na Din-din-din”, sanarwar ta bayyana haka.

Hukumar ta ce tana nan tana daukar matakan gaggawa don warware korafe-korafen wadanda suke cewa ba su samu katinansu ba, ta kuma sha alwashin warware matsalar kafin wa’adin karbar Katinan ya kare.

Daga karshe sanarwar ta ce: “Muna so mu nanata cewa bayan wa’adin Litinin, 11 ga watan Fabrairu, 2019, dukkan Katinan Zabe na Din-din-din da ba a karba za a tattara su a kuma jibge su a Babban Bankin Najeriya, CBN, don ajiyewa har sai bayan manyan zabuka lokacin da karbar katinan da kuma ci gaba da yi wa masu zabe rijista zai ci gaba”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan