Kun taɓa ganin Buhari yana ƙwallo?

134
Shugaba Muhammadu Buhari

Jaridar The PUNCH ta wallafa wani hoto da aka dauki Shugaba Muhammadu Buhari yana tamaula tare da matasa magoya bayansa.

Yanayin dai ya yi kama da wani taro, inda yake a matsayin bako a wajen.

Amma ba kamar yanayin da aka saba gani ba, inda ake ganin dan kwallo yana sanye da kayan wasa, an ga Shugaban Kasar a wannan hoto sanye da Babbar Riga da hula.

Shugaban Kasar ya yi kamar alkalin wasa ko mai tsaron raga da hula wanda a zahiri yake kokarin fara tamaular, ya daga ta sama da kansa, ya yi kamar mai nazarin yadda yanayin yake kafin ya jefa tamaular.

Ma’abota amfani da kafafen sada zumunta na zamani su yi ta mayar da martani akan wannan hoto.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan