Babban Dalilin da yasa ake shaye-shaye da yadda yake jawo koma baya ga Al’umma

350

Shan Kwaya wata babbar matsala ce ga rayiwar Matasa a yau, Kuma matsala ce wadda take taba ko wanne fanni na rayiwa.

Abin mamaki ga shaye -shayen miyagun kwayoyi matsalace wacce ko wanne irin mutun ya shiga ciki misali mai wadata yanayi, talaka yanayi, babba yanayi yaroma yanayi kuma daga ciki duk wanda yakeyi yanayi ne a sirri gudun kada a ganshi duk da yana sane da cewa ba abu bane mai kyau. Amma duk da haka Al’umma suna daukar kudinsu suna siyan abinda zai basu matsala ga lafiyarsu, duk da cewa muna sane da cewa lafia itace kan gaba a jin dadin rayiwa, amma duk da haka bama gane cewa kanmu muke chutarwa ta hanyar shaye-shaye.

Masana da yawa sunyi banayi akan illar shan miyagon kwayoyi Masani (Laver 1978), ya kalli shan kwaya ko ganye da rashin tsari ga Al’umma kuma yace babbar matsala ce wadda take haifar da Kansa yace in Al’umma basu kiyaye ba to daga lokacin da suka bari matsalar da ci gaba, to zai shafi zamantakewa.

Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa wata babbar Matsala ce wadda take tun karo mu a zamantakewarmu ta yau da kullum, kuma wata babbar matsalace ga matasa.A Nigeriya, misali jahar Kano ita ce jihar da tafi ko wacce yawan matasa masu shaye-shaye binciken hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA 2013), ita ce ta fitar da wannan binciken kuma tace wanda suke fama da matsalar shaye-shayen matasa ne. Tace matasa sun ne shugabannin gobe, lalle ba a sami shugabanni ba a gobe indai a haka matasa zasu tafi suna shaye-shayen kwayoyi indai a tsawan rayiwarku zaku tafi da wannan dabi’a.

duk da cewa ina sane da cewa masu shaye -shaye sunayi ne saboda hujjoji da ban daban wasu suna yi ne saboda su sami karfi a aikinsu misali, mai talla, mai aikin gini, direba da sauran masu yin aikin karfi duk da haka wannan bahagon tunanin naku ba dai dai bane ga lafiyarku.

Masani (Earl 2000). Ya kalli wannan dabi’a na rashin sanin rayiwa, inda masanin yayi bayani dalla-dalla akan sakamakon shaye-shaye.
Inda yace duk mutumin da ya jefa kansa cikin wannan yanayi to akwai barazanar rasa aikinsa ko kora daga makaranta karshe yazo ya tsinci kanshi a gidan Yari.

Akwai manyan matsaloli da muke kallo wanda suke jefa matasa ga dibi’arnan ta shaye- shaye misali rashin ilimi, talauci, da kuma matsugunnin da matasa suke samun kansu, kamar unguwar da ake kira kazo nazo yayin da mutane suke chunkushe a waje daya kowa da tunaninsa kuma kowa da Al’adarsa sanan kowa da yaransa. Babban abin dubawa anan shine duk lokacin da matasa suka tsinci kansu a irin wanna yanayin to akwai barazana ga tarbiya. Rukunin abokai sune suke jefa Al’umma ga Dabi’arnan ta shaye-shaye.

Kowa wacce Al’umma akwai rawar da zata iya takawa wajan dakile wannan dabi’a mara kyau. Duba da yadda muke rayiwa yau a. Nigeriya rayiwa mukeyi ta cewa in jifa ya tsallake kanka to ya fada kan kowa wannan magana kuskure ce, domin jifanan da ake magana in ya tsalle ke kanka to lallai zai dawo maka domin kuwa in kana takama baka shaye – shaye kuma kana kyamatarsu to wanann ba karamar bara zana bace ga kowacce Al’umma domin kuwa in ba kasha to kaninka yana sha ko yayanka yana sha duk in, ka tsira daga wannan to lalle makocinka yana fama, da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Wanda wannan shaye -shaye da muke magana yana da salo me tarin yawa in ka magance wannan sai kaga wannan domin duk mutumin da zai yi bincike akan wannan Dabi’a ta shaye -shayen miyagun kwayoyi ko saka makonsu ga lafiyar matasa to lalle ya dauko babban aiki wanda bashi da karshe a kusa.

Ta’amulli da miyagun kwayoyi wata babbar hanyace wadda matasa suke bi domin rage tsawar rayiwarsu a duniya, domin kuwa duk wanda yake cikin wannan masifa da ya dorawa kansa wata hanyace mafi sauki na ragewa kansa kwanaki a duniya. Amma da yawa bamusan haka ba, kuma matsalar ko yaushe kara ya duwa take a tsakanin matasa masu karancin shekaru.

Domin kuwa mutane da yawa suna buguwa su kai kansu ga halaka, bayan haka wannan dabi’a itace wanda matasa suke aikata manyan laifuka kamar: kisan kai, fashi da makami, fyade da sauran manyan laifuka wanda da yawa masu aikatasu matasa ne kuma suna aikata laifin ne sakamakon shan miyagun kwayoyi.

Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com
08037340560 (Text Only)

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan