Zaɓe: Buhari da Atiku za su sanya hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta karshe

169
Buhari da Atiku

An bada sunan tsohon Shugaban Amurka na 42, Bill Clinton da Sakatare Janar na Kungiyar Kasashen Rainon Ingila, Baroness Partricia Scotland a matsayin manyan baki da za su jagoranci bikin rattaba hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya.
Za a gudanar da rattaba hannun ne a Dakin Taro na Kasa da Kasa dake Abuja ranar Laraba, 13 ga Fabrairu, 2019.

Wadanda suka tsara wannan sa hannu sun ce Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP za su gana da tsohon shugaban na Amurka.

Wata sanarwa daga Shugaban Sakatariyar Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa(Cibiyar Kukah), Fr Atta Barkindo ta ce manufar sa hannun ita ce a sa ‘yan takarar shugabancin kasar su karbi sakamakon zaben matukar dai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ce ta sanar da shi.

“Yayinda muke kara kusantar zabukan kasa na Najeriya, dole mu dauki barazanar rikicin siyasa da gaske”, a cewar Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa, NPC.

“Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa yana sane da muhimmancin yin zabuka da mika mulki cikin lumana, ya tataro masu ruwa da tsaki da yawa don shirye-shirye zaben 2019.

“A wannan gaba, yana so ya sanar da cewa ya gayyaci Shugaban Amurka na 42, Bill Clinton da Sakatare Janar na Kasashen Rainon Ingila Baroness Partricia Scotland don su ziyarci Najeriya daga 12 zuwa 13 ga watan Fabrairu, 2019 gabanin zabukan shugaban kasa”, in ji Mista Barkindo.

“Tsohon Shugaba Clinton da Baroness Scotland za su gabatar da sakonnin fatan alheri a bikin sa hannu ga Yarjejeniyar Zaman Lafiyar ta Kasa wanda za a yi A Dakin Taro na Kasa da Kasa dake Abuja ranar 13 ga watan Fabrairu”, sanarwar ta kara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan