Hukumar Bada Katin Zama Dan Kasa, NIMC hukuma ce da aka kafa ta don tattara bayanan ‘yan kasa tare da adana su.
Hukumar NIMC tana gudanar da rijista ga jama’ar kasar nan ta hanyar samun sahihan bayanasu da take amfani da su don bada shedar zama dan kasar.
Hukumar na samun wadannan bayanai ne ta hanyar takardun sheda da ake nunawa a lokacin rijista kamar shedar haihuwa, da ta zama dan wata karamar hukuma ko kabila da sauransu. Kuma da su take amfani don bayar da katin da ake kira National Identity Card, wato Katin Shedar Zama Dan Kasa.
Bayan an yi wa mutum rijista ana ba shi Katin Dan Kasa dake dauke da wasu lambobi guda 11 da ake kira da Nationa Identification Number wato Lambar Shedar Zama Dan Kasa.
Wadannan lambobi suna da muhimmancin gaske don da su ne ake amfani wajen shigar da bayanan mutum, kuma da su ne za a dinga amfani wajen duba bayanai a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. A takaice wadannan lambobi sune shedar mutum.
Wani abin lura a nan shi ne ba a canza wa mutum lambobin. Idan an yi wa mutum rijista kuma aka ba shi lamba ta NIN, to ta zama tashi har abada kuma a duk lokacin da ake bukatar bayani game da mutum, to da ita za a yi amfani. Yana da muhimmanci matuka mu adana katin mu na Dan Kasa don amfani da shi a harkokin rayuwa na yau da kullum.
Ga wanda bai yi rijista ba, yana da kyau ya garzaya zuwa ofishin Hukumar NIMC mafi kusa da shi don yin rijistar Katin Shedar Zama Dan Kasa saboda ta wannan hanyar ce kadai mutum zai samu cikakkiyar shedar zama dan kasa