Saura ƙiris Buhari ya sha jifa

46

Saura kiris Shugaba Muhammadu Buhari ya sha jifa a ranar Litinin a Filin Wasa na Kasa da na MKO Abiola dake Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun lokacin da wasu ‘yan daba suka jefi Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshimohole a yayin gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Taron, wanda aka fara jim kadan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Filin Wasa na Kasa da Kasa na MKO Abiola dake Kuto a Abeokuta an tsayar da shi na dan wani lokaci biyo bayan rikicin.

Rikicin ya barke ne lokacin da aka gayyaci Mista Oshimohole don ya gabatar da jawabinsa.

Yayinda ya fara jawabi, sai wasu mutane da ake zargin ‘yan daba ne suka fara jifan sa da duwatsu, kuma daya daga cikin duwatsun ya nufi inda Shugaba Buhari yake zaune.
Daya daga cikin jami’an tsaron dake tsaron Shugaban ya tare dutsen inda jifan ya same shi.

Al’amarin ya fusata jagororin jam’iyyar da suka hada da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu wanda ya bar filin taron lokacin da Shugaba Buhari ke gabatar da jawabinsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan