An gudanar da Bikin Bada Kyaututtuka na Grammy Awards Karo na 61

15

An samu sauyi a wurin bikin bada Lambar Yabo Karo na 61 na Grammy Awards.

A wannan karo an ba wa mata 38 lambobin yabo a fanni daban-daban. A bara, mata 17 ne suka samu lambar yabo daga cikin lambobi 86 da aka tanada.

Matar tsohon shugaban kasar Amurka, Michelle Obama ta halarci wurin taron inda ta jagoranci bada lambobin yabo ga matan da aka karrama. A tare da ita akwai mata da suka yi fice a sana’ar waka kamar su Alicia Keys da Jennifer Lopez da Jada Pickett-Smith da Lady Gaga.

Misis Obama ta yi jawabi akan muhimmancin da amfanin waka inda ta ce: “Waka na taimakawa wajen bayyana kanmu da mutuncinmu ko farin ciki ko bakin ciki ko burinmu na rayuwa ko abubuwan dake cikin zuciyoyinmu. A kowane baiti cikin kowace waka muna kara fuskantar juna, muna kira zuwa ga junanmu. Ni kaina wakka ta taimake ni a rayuwa”.

Daga nan mawakiya Diana Rose ta gudanar da wasa tare da jawabi da godiya ga masoyanta. Mawakiyar tana shirin bikin cika shekara 75 a duniya. A farkon taron, an karrama fitacciyar mawakiya Lady Gaga bisa rawar da ta taka a wani fim mai suna A Star is Born.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan