Ana sa ran warware rikicin APC a jihar Zamfara kafin zaɓe

166
Alamar jam'iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana fatan kawo karshen rarrabuwar kawuna da ya dabaibaye jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara tun lokacin da aka gudanar da zabukan fitar da gwani a jihar.

Shugaban ya bayyana haka a lokacin da yake gudanar da yakin neman zabe a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, ya yi alkawarin kare kundin tsarin mulki da sashin shari’a, kuma yana nan kan bakansa. Jihar Zamfara na daga cikin jihohi takwas da jam’iyyar APC ta fuskanci kalubale yayin zabukan fitar da gwani.

Shugaban Kasar bai daga hannun kowanedan takara ba, saboda kotu tana kokarin tantance dan takarar da ya dace.

Ya ce ya cika wa al’ummar kasar nan alkawarin da ya dauka a shekarar 2015 akan bangarorin tsaro da ci gaban tattalin arzikin kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Ya kare jawabin da kira ga al’umma da su fito domin zaben ‘yan takarar jamiyyar APC a babban zabe mai karatowa kuma su kasance masu bin doka a lokutan zabe.

Kafin jawabin shugaban kasa, gwamnan jihar, Abdulazeez Yari, ya yi wa shugaba Buhari godiya bisa wannan ziyara tare da jaddada wa jama’a cewa kotu za ta yi musu adalci wajen umartar hukumar zabe barin dan takarar jam’iyyar shiga zabe.

A nashi jawabin, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bukaci yan jam’iyyar su kasance masu bin doka don jam’iyyar ta samu nasara a babban zabe.

Wadanda suka yi wa shugaban kasar rakiya akwai Ministan Tsaro,Mansur Dan Ali da Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurrahman Dambazau da tsofaffin gwamnonin Zamfara, Borno da Sokoto.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan