Ba wata jikakkiya tsakanina da Buhari- Shekarau

215
Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, tsohon Ministan Ilimi kuma dan takarar sanata a Kano ta Tsakiya karkashin tutar jam’iyyar APC, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ba wata jikakkiya tsakaninsa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ranar Talatane lokacin da yake bada amsar wata tambaya da aka yi masa yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano.

“To ina ganin, da farko dai ba gaskiya ba ne cewa akwai akwai wata jiƙaƙƙiya wai tsakanina da Shugaban Kasa, Janaral Muhammadu Buhari. Kusan, wato mutane ne suke kitsa wadannan al’amura. Tun da muka zo cikin jam’iyyar ANPP, har ya fita ya zama CPC dinsa, har muka gama gwamnati aka zo aka sake haduwa, WalLahi iya sanina, ni dai ni da shi bai taba gayan min ga wani abu da ya shiga tsakani ba, ni ma ban taba sanin ga wani abu da ya shiga tsakani ake wani ja-in-ja ba”, in ji Mista Shekarau.

Malam Shekarau ya ce mabiya ne suke haddasa fitina, kuma suna da dalilansu na yin haka.

“Wato masu biyayya suna da dalilansu na haddasa fitina, na fadar abinda babu shi”, a kalaman Malam Shekarau.

Ya kara da cewa su uku suka jagoranci hadakar jam’iyyun da suka kafa APC. Ya ce shi daga ANPP, Tom Ekemi daga ACN, sai marigayi tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi Garba Gadi daga CPC.

Malam Shekarau ya ci gaba da cewa ba zai iya tuna sau nawa ya je gidan Shugaba Buhari ba a lokacin da ake yunkurin kafa jam’iyyar APC.

Malam Shekarau ya ce lokacin da ya bar APC ya koma PDP ba maganar Buhari ba ce ba maganar wani ba ce, ya ce magana ce ta cikin gida.

“Mu da wadanda suka shigo ba a samu fahimtar da muke nema ba da kuma wato yadda da al’amuran da muka bijiro da su”, a kalaman Shekarau.

Malam Ibrahim Shekarau ya ce tun bayan dawowarsa APC, ya halarci tarukan ganawa da Shugaba Buhari kusan sau uku ko sau hudu, kuma ko yaushe ana gaisawa cikin raha da fahimtar juna.

“Kunnena ni dai bai jiye min wani abu na sabani a ce ko daga gare shi ko daga wani na kusa da shi, amma masu karyar suna tare da shi za su iya fadar duk abinda za su fada.

“Amma dai a takaice, ba wani zaman doya da manja ni da shi. Kuma Allah cikin hikimarSa in shaa Allahu za ma mu zo mu yi aiki tare, domin Shugaban Kasa mafi kusacin abokan aikinsa su ne ‘yan Majalisar Dattijai da na Tarayya sama ma da ministoci da yake nadawa. Domin mu za mu zama abokan aikinsa na ala tilas, domin ‘yan majalisa da gwamna ko shugaban kasa abokan aikinsa ne na ala tilas domin kowannensu zabo su aka yi.

“Kuma wannan ta sa tilas za mu yi aiki tare, dama kuma akwai fahimtar juna, saboda haka babu wani zaman doya da manja, ni dai iya sanina iya fahimtata babu wani sabani kuma in shaa Allahu za mu zo mu yi aiki tare cikin fahimtar juna”, Malam Shekarau ya kara da haka.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Hi. I have checked your labarai24.com and i
    see you’ve got some duplicate content so probably it is
    the reason that you don’t rank high in google. But you can fix this
    issue fast. There is a tool that generates content like human, just search in google: miftolo’s
    tools

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan