Kotu ta raba auren wasu ma’aurata sakamakon bambancin addini

154
Gudumar Alƙali

Alkalin Kotun Al’ada dake Ibadan, babban birnin jiharhar Oyo, Cif Ademola Odunade ya raba auren wani mutum mai suna Azeez Muritala da wata mata mai suna Ramota bayan sun shafe shekaru 31 tare.

A karar da ya shigar, Mista Azeez ya bukaci kotun ta raba aurensa da matar tasa bayan da ya gano tana wani addinin daban ba Musulunci ba.

Ya ce ya gaji da hakuri da sa ran za ta canza hali duk da cewa ya aure ta tun a shekarar 1988 don ta yi masa alkawarin musulunta.

Ya kara da cewa, bai san halin da matar tasa take ciki ba, saboda ta daina tuntubarsa akan komai a natsayinsa na mijinta. Bugu da kari, ta fara addinin Kiristanci tare da nuna wasu dabi’u da bai gamsu da su ba.
Ya kara da cewa daga baya kuma sai ta fara sa ma yaransu tsanar sa ta hanyar ce musu shi mugu ne.

A cewarsa, hakan bai ishe ta ba, sai ta kwashe ‘ya’yansu uku ta gudu da su ba tare da saninsa ba. Wasu kwanaki bayan haka, sai ta yi kokarin dauke ragowar da dayan da ke hannunsa. Ganin irin take-takenta, sai ya kai karar ta wajen magabatanta amma sai suka bashi hakuri tare da alkawarin cewa za ta canza.

Wadda ake kara, Ramota ba ta musanta zargin da ake mata ba amma ta ce da yardarsa take zuwa coci, domin yin ibadar,ta kuma ce ita ba ta gudu da yaransu ba, su suka biyo ta da kansu saboda mahaifinsu ba shi da lokacinsu.
Daga karshe, Kotun ta raba auren mai shekaru 31 kuma ta mika yaran hudu hannun mahaifinsu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan