Buhari da Atiku sun kara sa hannun a Yarjejeniyar Zaman Lafiya

151
Shugaba Buhari, Abdulsalam Abubakar da sauran mahalarta a wajen sa hannu akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP suka sake sa hannu akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya.

Idan dai za a iya tunawa, wannan kafa ta kawo rahoton dake cewa a ranar Laraba (yau), 13 ga watan Fabrairu, 2019 ne aka tsara sa hannu a wannan yarjejeniya.

An gudanar da sa hannun ne a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa dake Abuja.

Wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban mulkin soja na kasar, Abdulsalam Abubakar, Mathew Kukah da Partricia Scotland, Sakatariyar Kungiyar Kasashen Rainon Ingila.

Rahotanni sun ce wannan shi ne karon farko da ‘yan takarar biyu suka hadu tun bayan da jam’iyyunsu suka tsayar da su a matsayin ‘yan takara.

Duka ‘yan takarar sun yi kira ga magoya bayansu da su zauna lafiya.

Kwamitin Tabbatar da Zaman Lafiya da Cibiyar Kukah ne suka shirya wannan sa hannu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan