Kotun Ƙoli ga jam’iyyar APC a Rivers: Ba ki da ‘yan takara

140
Alamar jam'iyyar APC

A ranar Talata ne Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin cewa jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ba ta da ‘yan takara a jihar.

Kotun ta amince da korafin da wasu mambobin tsagin jam’iyyar suka shigar gabanta. Ta ce zaben fitar da gwani na ‘yan takarar jam’iyyar batu ne na kafin zabe, kuma ya kamata a ce an gabatar da karar tuni.

Dama tuni wata Babban Kotu ta soke zabukan fitar da gwani da jam’iyyar APC reshen jihar Rivers din ta gudanar sakamakon rikicin da ya dabaibaye zaben.

Bayan nan ne jam’iyyar APC reshen jihar ta garzaya Kotun Koli don kalubalantar wannan hukunci, inda ranar Talatar nan kuma Kotun Kolin ta tabbatar da hukuncin Babban Kotun.

Hakan dai na nufin jam’iyyar APC ba ta dan takara ko daya a jihar, ba kuma za ta iya shiga zabe ba.
Shugaba Buhari ya bayyana damuwarsa bisa wannan hukunci ranar Talata yayin gudanar da yakin neman zaben a jihar ta Rivers.

Shugaban ya ce ya damu sosai bisa cewa jam’iyyar ta APC ba za ta iya gabatar da ‘yan takara ba a jihar, ya ce amma kuma dole ya girmama doka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan