Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta bankado wani shiri da wasu bata gari ke yi don kawo cikas a zaben mai zuwa da za a yi ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, 2019.
Jami’in Hudda da Jama’a na Rundunar, SP Abdul Jinjiri ya sanar da haka a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
Ya bayyana cewa Rundunar tare da hadin gwiwar ‘yan uwanta hukumomin tsaro a jihar za su bankado wadanda ke shirin kawo cikas kafin, lokacin da bayan zabukan.
Sanarwar ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Sanarwar ta ci gaba da cewa za a hana zirga-zirga tun daga 12 na daren Juma’a, idan ba jami’an gwamnati da masu wani babban dalili ba ba a yarda a ga kowa akan titi ba ranar zabe.
Daga karshe Rundunar ta bada lambobin waya da al’ummar jihar za su iya tuntuba domin bada korafi game da harkokin tsaro ko neman karin bayani ranar zabe.
Lambobin su ne:
08075391069, 08057100000, 08088520528, 08088517047, 08166223705, 09030622111.