Za mu yi awon gaba da duk mai shirin aikata laifi lokacin zabe- Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano

180
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Wakili Muhammad

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Wakili Muhammad ya bayyana cewa jami’ansa za su yi awon gaba da duk wani wanda aka samu yana kokarin tayar da hatsaniya a lokacin gudanar da zabe ko bayan an kammala a jihar.

Kwamishinan ya bayyana haka ne yau a cikin shirin Barka da Hantsi na gidan Radio Freedom.

Kwamishinan ya bayyana cewa rundunarsa ta samu nasarar cafke ‘yan bangar siyasa 450 a jihar ta Kano a wannan makon, kuma an kama su dauke da makamai a gurare daban-daban a yakin neman zabe.

Haka kuma, ya yi kira ga iyaye da su kasance masu sa ido akan ‘ya’yansu don gudun mu’amala da gurbattatun mutane.

Daga karshe ya ce sun ba wa jami’ansu horo na musamman don ganin sun kula da rayukan al’umma da lafiya da kuma walwalarsu a yayin gudanar da zabe.

Kwamishinan ya yi kira ga jama’a da su hanzarta kai wa jami’ansa rahoton duk wani ba dai-dai ba da suka ga ana aikatawa ta wannan lambar waya: 08162325501.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan