Ƙuri’arka ‘Yancinka

40
Ƙuri'a

kuri’arka ‘Yancinka

A yau da ake jajibirin zabe, shirye-shirye sun gama kankama domin kada kuri’ar zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisun Dokoki da na Dattijai a gobe Asabar, 16 ga watan Fabrairu, 2019.

Bayan nan sai a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 2 ga watan Maris, 2019.
Yana da kyau al’ummar kasan nan su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’a, yin hakan zai taimaka matuka wajen hana magudin zabe a zabubbukan da za a gudanar. Hakan kuwa zai samu ne idan aka samu hadin kai a tsakanin hukumomi da al’ummar da abin ya shafa.
Wabi babban abin jan hankali a nan shi ne, ya kamata ma’aikatan Hukumar Zabe da jami’an tsaro, su zama masu yin aiki da gaskiya ba tare da son zuciya ba. Sannan jam’iyyun siyasa su turo wakilai na gari wanda za su taimaka wajen ganin an gudanar da zabe cikin lumana a rumfunar zabe.
Wani abin farin ciki shi ne ganin yadda kasashen duniya suka hallara don sa ido akan zaben da za a yi a kasar nan. Hakan zai taimaka gaya wajen sa ido akan ‘yan siyasa masu niyyar siyan kuri’u, ko satar su ko tada hatsaniya. Zuwan kasashen duniya bai zai shafi gudanar da zaben, ba amma hakan zai zama kariya ga rigingimun zabe da ka iya tasowa.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta lashi takobin gudanar da zabe mai inganci cikin gaskiya da adalci.
Hukumar ta ce ta yi wa mutum 84,004,84 rijista, kuma za a kada kuri’u a rumfunan zabe 199,973 dake fadin kasar nan.

Turawa Abokai

3 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan