Abubuwa 3 da kafafan yada labarai zasu yi don taimakawa ayi zabe cikin lumana

215
Buhari da Atiku

Ƙungiyar Konrad-Adenauer-Stifing (KAS) ta kasar Jamus ta bukaci yan jarida da su kasance masu kawo rahoton gaskiya a lokacin gudanar da zabe a kasar nan. Wakilin kungiyar da ke kasar nan, Dr Vladamir Kreck ne ya bayyana hakan a hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a garin Abuja.

Kalolin kuri’u da kalolin akwatinan zaɓe

Dr Vladamir yace kafafan yada labarai zasu taka muhimmiyar rawa wajen ganin anyi zabe mai Inganci cikin gaskiya da lumana ta hanyar sa ido da kawo rahotonin abubuwan da ke gudana sannan kada rahotonin su zama masu fifita wani dan siyasa ko wani bangare.

Daga karshe yayi kira ga yan takarkaru da su karbi sakamakon zabe gobe asabar cikin lumana kuma su nemi hakkin su a kotu a inda suke zargin ba’a yi musu adalci ba. Ga jama’ar kasa, yace su kada zabe cikin kwanciyar hankali da lumana kuma su kada zaben bisa cancantar yan takarar gare su.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan