Da ɗumi-ɗumi- Ta yiwu a ɗaga zaɓe

156
Shugaban Hukumar Zaɓe, Farfesa Mahmud Yakubu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC na duba yiwuwar daga zabukan shugqaban kasa da na ‘yan Majalisun Tarayya da aka shirya gudanarwa a gobe Asabar, a cewar jaridar Premium Times.

Majiyoyi da dama da suke da kusanci da Hukumar sun ce ta yiwu a ɗaga sakamakon kalubale da Hukumar ke fuskanta a jihohi da dama.

Jihohin sun hada da Ekiti da Naija.

Majiyar Premium Times ta ce Kwamishinonin INEC na can na ganawa a Hedkwatar INEC dake Abuja.

A ranar Juma’a da daddare ne ake sa ran samun bayani a hukumance.

Ku biyo mu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan