Ko kun san kalolin kuri’u da kalolin akwatinan zabe

182
Kalolin kuri'u da kalolin akwatinan zaɓe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana kalolin akwatinan zabe da za a yi amfani da su gobe Asabar yayin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalissun tarayya.

Shugaban Sashin Wayar da Kan Jama’a na Hukumar Zaben na jihar Anambra, Mista Leo Nkedife ne ya bayyana haka ga kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN a Awka, babban birnin jihar Anambra ranar Alhamis.

Mr Leo ya kara da cewa za a yi amfani da jar takardar zabe da kuma jan akwatin don zaben shugaban kasa. Sai bakar takardar zabe da bakin akwatin don zaben sanatoci, sannan sai koriyar takardar zabe da koren akwatin don zaben ‘yan Majalisar Wakilai.

Ya ce Hukumar Zabe ta bayyana kalolin ne don kara wayar da kan al’umma game da zaben da zai gudanar a gobe Asabar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan