Home / Cigaban Al'umma / Jawabin Shugaba Buhari kan kashe-kashen da aka yi a Kaduna

Jawabin Shugaba Buhari kan kashe-kashen da aka yi a Kaduna

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa bisa kisan da aka yi a jiya juma’a a karamar hukumar Kajuru da ke jihar kaduna. Shugaban ya bayyana hakan ne ta hannun maimtaimakinsa na musamman akan harkokin yada labarai malam Garba Shehu. Ya kara da cewa jami’an tsaro zasu yi bincike kuma duk wanda ke da hannu a wannan , to gwamnati zata hukunta shi.

Jami’an tsaro
Shugaban yace, yin hakan ba zai janye hankalin kasarnan daga kan zabukan da za’a gudanar ba, gwamnatinsa a shirye ta ke don kawar da duk wata matsala da zata shafi zaben.

A jiya ne, gwamnatin jihar kaduna ta bayar da sanarwan wasu yan bindiga sun hallaka mutum 66 a rugagen fulani dake Maro Gida da Iri a karamar hukumar Kajuru. An kashe yara 22 da mata 12 sai mutum hudu da suka jikkata.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i
Gwamnati tayi ta’aziyya ga iyalan wanda abun ya rutsa da su, tare da gargadin su akan daukan fansa. Zuwa yanzu an zuba jami’an tsaro a wurin da abin ya auku.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *