INEC ta bada izinin ci gaba da yaƙin neman zaɓe

32
Tambarin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce a halin yanzu jam’iyyu za su iya ci gaba da yaƙin neman zaɓe biyo bayan dage zaɓen da ta yi.

A ranar Asabar Hukumar Zaben ta bakin Shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu ta sa takunkumin ci gaba da yakin neman zabe bayan ta dage zaben da ta yi daga 16 ga watan Fabrairu zuwa 23 ga watan Fabrairu.

Tun a wancan lokaci, jam’iyyun APC da PDP sun ce ba za su bi wancan umarni na hana yakin neman zabe ba.

Dukkan jam’iyyun biyu sun ce matsayin na Hukumar Zabe ya saba wa dukkan dokokin kasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan