Kamfanina layin sadarwa na waya 9mobile ya kaddamar da wani shiri ga abokan cinikinsu mai suna Magic Hour Promo, inda kamfanin zai ba miliyoyin jama’a dake amfani da layinsu kyaututtuka a tsawon watanni uku.
Shirin ya fara aiki da 11 ga watan nan kumma za’a dauki tsawon kwana 90 ana bada kyaututtuka da suka hadar da kira a kyauta (free airtime), smart Phonea da tsabar kudi. Kamfanin yayi hakan ne don godewa abokanan cinikinsu na amfani da layinsu na tsawon lokaci.
Mataimakin shugaba a bangaren kasuwanci na kamfanib, Mr Adebisi Idowu ya bayyana cewa kowani abokin ciniki zai iya shiga tsarin ta sanya mafi karancin kudi naira 100 a wayarsa ko kuma mutum ya aika sakon WIN ga 88808 don kara samun dama a gasar. Akwai babban kyauta ta naira miliyan 20 ga mutum daya, da naira miliyan biyar kowanni wata ga mutum daya, da naira dubu 250 kowanni rana har kwana 20, da naira dubu 50 ga mutum biyar a kullum, sai wayar smart phone guda biyar a kowanni sati.
A satin da ya gabata ne, kamfanin na 9mobile ya kaddamar da wannan gasa a Arewacin kasarnan a jihohin Adamawa, da Bauchi, da Borno, da Gombe, da Jigawa, da Kano, da Katsina, da Taraba, da Yobe.