Abubuwa 7 da Mutum zai yi don samun Visa a Sauƙaƙe

63

Jama’a da dama kan tsinci kansu a tsaka mai wuya a lokacin da suke kokarin samun takardar izinin shiga wata kasa watau Visa. Hakan yana faruwa ne sakamakon rashin sanin abin da ake bukata a wajen mutum a lokacin da yaje neman takardar Visa.

Abin lura a nan shi ne, ya kamata duk mai neman takardar Visa ya zama yana da cikakkun takardun shaida, sannan ya zama mai kwarin gwiwa. Hakan na taimakawa matuka wajen saukake wahalhalun da jama’a da dama ke fuskanta. Ga abubuwa bakwai da mutum zai yi don samun sauki a wajen yin Visa.

Yin bincike kafin zuwa:
Yana da kyau mutum yayi bincike kafin zuwa neman takardar Visa don gudun bada amsar da bata dace ba ga tambayoyin da za’a yi. Sannan irin tambayoyin da za’a yi na taimakawa wajen bada amsar da ta dace.

Ban da karya ko kin amsa tambaya:
Hukumomi suna tambayoyi a lokacin bada takardar Visa don sanin mutum da fahimtar sa, amsa musu tambayoyi da karya ko kin amsawa baki daya na iya jawo matsala.

Zuwa da cikkakun Takardu:
Mutum ya guji zuwa ba tare da takardun shaida cikakku ba. Tabbata duk wata takardar da zasu bukata mutum na tare da ita.

Amsa tambaya a takaice: Babu amfanin fadi ba’a tambaye ka ba. Yana da kyau mutum ya amsa musu tambaya a takaice ba tare da dogon jawabi ba.

Zuwa a kan lokaci:
Mutum ya zama mai daraja lokaci. Kada mutum ya makara domin makara na nuna ba’a dauki lokacinsu da muhimmanci ba.

Yin shiga ta kamalaAmincewa da kai:
Ka da kyau mutum ya kasance cikin juyayi da dar-dar. Hakan zai iya karya kwarin gwiwa tare da sa tsoro a cikin zuciya. Wannan zai iya jawo rudewa, kuma hakan ka iya sawa a hana mutum takardar Visa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan