Umarnin kashe masu satar akwatin zabe: ADC ta mayar da martani ga APC

132
Alamar jam'iyyar ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da cin zarafin jam’iyyun adawa da barazanar kisa ga yan Najeriya, inda ta ce dole gwamnati ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka a lokacin zabe, ba ta yi sanadin salwantarsu ba.

A sanarwar da Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Alhaji Sa’id Abdullahi da Sakataren Jam’iyyar, Ralphs Nwosu suka sanya wa hannu bayan gama taron gaggawa a Akwa dake jihar Anambra, sun nuna kin goyon bayansu ga kalaman da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ga jami’an tsaro na su nuna rashin imani ga masu sace akwatin zabe.

Sanarwar ta ce jam’iyyar ta ADC ta janye matsayinta na farko inda ta bukaci Shugaba Buhari da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu su ajiye mukamansu, ta yi kira ga shugaban kasa da shugabannin siyasa da su zama masu nuna misali na gari ga magoya bayansu musamman a kan lamarin zabe.

Daga karshe jam’iyyar ta yi kira ga magoya bayanta da su fito su jefa wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuri’unsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan