Gwamnatin Tarayya ta bayyana Juma’a, 22 ga watan Fabrairu, 2019 a matsayin ranar hutu don zabukan shugaban kasa da na ‘yan Majalisun Tarayya da za a yi ranar Asabar, a cewar rahoton jaridar Vanguard.
Sanarwar hutun ta fito ne daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida wadda wadda Abdurrahman Bello Dambazau ke jagoranta.
Amma Gwamnatin Tarayyar ta ware ma’aikatan bankuna da sauran ma’aikata da aikinsu ke da matukar muhimmanci daga hutun.
“Gwamnatin Tarayya ta bayyana Juma’a, 22 ga watan Fabrairu, 2019 a matsayin ranar hutu.
“An ware wadanda suke aiki mai matukar muhimmanci da ma’aikatan bankuna daga hutun.
“An bada hutun ne don ba ‘yan kasa damar komawa mazabunsu don zaben Shugaban Kasa da na ‘yan Majalisun Tarayya da aka sake shirya gudanarwa ranar Asabar.
“An umarci jami’an tsaro da su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a kafin, lokacin da kuma bayan babban zaben”, a cewar sanarwar.