Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta ƙaddamar da sabon Kamfanin Zirga-Zirgar Jiragen Sama

65
Jirgin saman Ibom Air a lokacin da aka ƙaddamar da shi a Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Obong Victor Attah dake Uyo ranar Laraba

A ranar Laraba ne Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta kaddamar Ibom Air, Kamfanin Zirga-Zirgar Jiragen Sama mallakin jihar da jirage biyu.

A jawabinsa, Gwamna Udom Emmanuel ya bayyana kaddamar da sabbin jiragen saman a matsayin wata babbar nasarar gwamnatisa.

Gwamna Emmanuel ya ce shekarun jiragen shida kawai da kerawa, masu cin mutum 90 ne kuma na zamani ne kirar C-FWNK daga kasar Canada.
Ya ce gwamnatin jihar Akwa Ibom ita ce kadai gwamnatin da take da kamfanin jirgin sama mallakin gwamnatin jiha a kasar nan.

Ya tabbatar wa da al’ummar jihar Akwa Ibom cewa za a rika amfani da Ibom Air a matsayin kasuwanci.
Ya ci gaba da cewa Kamfanin Zirga-Zirgar Jiragen zai yi aiki a hanyoyi masu riba, kuma zai fi bada fifiko ga al’ummar jihar ta Akwa Ibom.

Gwamnan ya kara da cewa an fara yunkurin samar da Ibom Air ne tun a shekara ta 2016, inda ya ce sai yanzu ne aka yi nasara.

Shugaban Majalisar Dattijai, Dakta Abubakar Bukola Saraki ne ya jagoranci kaddamar da wadannan jirage a hukumance a Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Obong Victor Attah dake Uyo.

A jawabinsa, Shugaban Majalisar Dattijan ya yabi kyawawan dabi’un shugabanci na Gwamna Udom Emmanuel.
“A yau, muna murnar shugabanci, muna murnar kyawawan abubuwa da za su iya fitowa daga Najeriya. Muna murnar jajircewar cimma guri.

“Gwamnan ya samar da wani yanayi da mutane za su iya samun ayyuka. Muna alfahari da kai a iyalin PDP cewa kana daya daga cikinmu”, in ji Mista Saraki.

A jawabinsa shi ma, Shugaban Kamfanin na Ibom Air, Idongesit Nkanga ya ce ce Kamfanin na Ibom Air zai fara aiki a kasa da kasa kafin karshen wa’adin mulkin Gwamna Udom Emmanuel.

Ya ce idan ya fara aiki ka’in da na’in, Kamfanin zai samar da ayyukan yi ga mutane 300.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ce jirgin farko ya taba kasa da misalin karfe 1:40 na rana yayinda jirgi na biyu ya taba kasa da misalin karfe 1:49.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan