Mutane Da Dama Sun Mutu A Lokacin Da Aka Kaiwa Tawagar Sanata Kwankwaso Hari

172
Tawagar Kwankwaso

Wasu rahotanni da muka samu yanzu sun bayyana cewa wasu matasa yan daba sun kai wa tawagar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a daidai kauyen Kofa cikin karamar hukumar Bebeji ta jahar Kano.

Rahotannin sun ƙara da cewa an samu hasarar rayuka da dama tare kuma da motoci sama da arba’in.

Sai dai wasu majiyoyi sun danganta faruwar lamarin da ‘yan dabar da dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa ya debe domin su tare tawagar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan