Jam’iyyar PDP a jihar Ogun bisa goyon bayan Babban Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Kasa ta dakatar da Segun Sowonmi, Kakakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Atiku Abubakar, dan takarar mataimakin gwamna a jihar, Dakta Reuben Abati da wasu mambobi 37 sakamakon zargin su da aikace-aikacen da suka saba wa jam’iyyar.
An sanar da dakatarwar ne a cikin wani jawabin bayan taro ranar Alhamis.
Jawabin bayan taron da tsagin Sikirulahi Ogundele ya sanya wa hannu ya dakatar da mambobin tsagin da Bayo Dayo ke jagoranta, ya kuma amince da ‘yan takarar majalisun jihar da na Majalisun Tarayya.
Mista Ogundele ya ce an amince da dakatar da mambobin da abin ya shafa ne a hukumance yayin wani taron ganawa na jiha da jam’iyyar ta yi a Legacy House dake Onikolobo a Abeokuta.
Ya ce wadanda aka dakatar din ba su zo sun kare kansu ba lokacin da aka bukaci su yi hakan.
Ya kara da cewa an samu mambobin da laifuka da dama da suka hada da kirkirar wani tsagi a jam’iyyar da yake kalubalantar shugabancin Jam’iyyar na Kasa karkashin jagorancin Prince Uche Secondus, yin wasu bayanai a kafafen watsa labarai wadanda ka iya zubar da kimar jam’iyyar da kuma shirya da halartar taruka da suka saba wa doka.
Banda Abati and Sowunmi, sauran wadanda aka dakatar su ne Sosanwo Adeola Ayoola, Odunjo Odunlaye Abiodun, Apostle Biodun Sanyaolu, Taiwo Shote, Segun Showunmi Anthony, Abimbola Lanre Balogun, Sunmonu Monsuru Olusegun, Kojeku David Sunday, Ajose Paul, Adesina Lateef, Adekoya Adesegun, Lawal Alaba, Azeez Ola Ogedengbe da Adisa Akintomiwa.
Haka kuma daga cikin wadanda aka dakatar din da akwai Biliaminu Owolabi, Sakiru Oladimeji, Babatunde Tajudeen, Wasiu Boladale, Samuel Adeyemi Ope-Ifa, Sunmonu Kayode, Taiwo Akinfenwa, Awojope Alao, Adebayo Benjamin, Bayo Raphael, Abiodun Sylvester Niyi, Segun Oduniga Kaka, Seun Adesanya, Awoyemi Olusegun Afolabi, Adeluyi Solola, Hassan M. A. Olajide and John Tosin Oludoyin, Fatai Adebimpe, Babatunde Sikirulahi, Okulenu Ojonla M., David Tayo Oluwole, Ayomide Babatunde, Kalejaiye Sunday Idowu da Akinsonwon Adekunle.
Jawabin bayan taron ya kara da cewa: “An dakatar da wadannan mambobi har sai kwamitocin ladabtarwa da jam’iyyar ta kafa sun gabatar da rahotanni”