Rikicin Kajuru: Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ya yi ƙarin haske

152

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman ya ce gwamna Nasir El-Rufa’i ya yi kuskure a maganar da ya yi na kashe-kashe da ya faru a karamar hukumar Kajuru a farkon wannan wata.

Kwamishinan ‘Yan Sandan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a kan batun yawan mutane da Gwamna El-Rufa’i ya ce an kashe a lokacin da rikici ya barke tsakanin Adara da Fulani a karamar hukumar Kajuru tare da bayyana cewa kashe-kashe ba Fulani kadai ya shafa ba.

Mista Abdurrahman ya shawarci Gwamna El-Rufa’i da ya daina furta yawan mutane da aka kashe a rikicin har sai an gama bincike.

Ya kara da cewa ana zargin rigimar ta faru ne sakamakon harin da Fulani suka kai wa Adara, sai su ma Adara suka dauki fansa a kan Fulanin.

Yanzu haka dai Rundunar ‘Yan Sandan ta kama daya daga cikin Fulanin da ake zargi da fara kai harin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan