Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ce zaman lafiya ya dawo a garin Kofa dake karamar hukumar Bebeji, bayan rigimar da ta barke a tsakanin mabiya jam’iyyar PDP da APC a jiya Alhamis.
Mai magana da yawun hukumar DSP Abdullahi Haruna ne ya yi karin bayani a kan faruwar lamarin inda ya ce an tura jami’an tsaro kuma sun shawo kan rigimar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya bada rahoton cewa rigimar ta barke ne sakamakon wucewa da tawagar yakin neman zaben PDP ta yi ta ta inda wurin dandazon magoya bayan jam’iyyar APC suke da misalin karfe 2 na rana.
An samu kone-konen ababen hawa da yi wa jama’a da dama rauni sakamakon rikicin.
Zuwan jami’an tsaro a kan lokaci shi ya taimaka wajen takaita rikicin daga zama babbar rigimar siyasa.
Turawa Abokai