Ƴan Sanda Sun Azabtar da Ma’aikatan Zaɓe da Hayaƙi Mai Sanya Hawaye a Kano

223

A jiya da daddare ne wasu Ƴan Sanda suka turnukawa ma’aikatan zabe na wucin gadi hayaƙi mai sanya hawaye a ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano. Lamarin dai ya faru ne a yayinda da hatsaniya ta kaure a dalilin nuna gajiya da jira ba tare da an saurare su ba.

Wani daga cikin ma’aikatan zaben ya shaidawa Majiyarmu cewa, “An bukaci da mu zo da wuri tun kamar karfe 10 am zuwa 3 pm ko kuma a sauya sunayenmu, amma sai dai abin ta kaice muna nan wurin har karfe 10 pm ba tare da wata magana kwakkwara daga INEC ba. Hakan ta sanya ma’aikatan korafi wanda daga bisani ya janyo daga murya da guna-guni.”

Majiyarmu ta rawaito cewa bayanda Ƴan Sandan suka ga abin na neman wuce makaɗi da rawa ne sai suka fara yunkurin kwantar da hankulan masu yiwa kasar hidima da sauran ma’aikatan zaben, amma yunkurin masu yaci tura. Nan take wani daga cikin jami’an ya laɓaɓo ya sirnana musu hayaƙim mai sanya idp hawaye.
Cikin lokaci ƙalilan mutane 3 suka fita hayyacinsu inda jariran da ake goye da su suka fara tsala kuka. “A cikin daren aka kai su babban asibitin garin na Kura.

Ƴan sanda da jami’an INEC duk sunƙi cewa komai dangane da faruwar lamarin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan