Bukola Saraki Ya Gaza Kai Bantensa

183

Shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki ya sha kaye a Kwara ta tsakiya da yake wakilta a majalisa.

Sakamakon wanda hukumar zabe ta sanar an tabbatar da Saraki ya faɗi a dukkanin ƙananan hukumomi huɗu da yake wakilta.

Dan takarar APC ne Ibrahim Oloriegbe ya kayar da Saraki a yankin Kwara ta tsakiya da ya kunshi kananan hukumomin Ilori ta yamma da Ilori ta Kudu da Ilori ta gabas da kuma Asa.

Bukola Saraki

Bukola Saraki na jam’iyyar PDP wanda kuma ya jagoranci yakin neman zaben Atiku ya samu jimillar kuri’u 68,994 a dukkanin kananan hukumomi hudu da yake wakilta.

Ibrahim Oloriegbe na jam’iyyar APC kuma ya samu jimillar kuri’u 123,808 a dukkanin kananan hukumomi hudu na Kwara ta tsakiya, sakamakon da ya ba shi nasarar doke Saraki.

(c) BBC HAUSA

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan