Dino Melaye Ya Lashe Zaɓen Sanatan Kogi

8

Hukumar zaben mai kanta ta ƙasa INEC reshen jihar Kogi ta bayyana Sanata Dino Melaye a matsayin mutumin da ya lashe zaɓen majalisar dattawan mai wakiltar Kogi ta Yamma.

Baturen zaɓen jihar, Farfesa Emmanuel Bala, ya bayyana cewa Sanata Melaye na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaɓen da ƙuri’a sama da 85,000.

Sanata Melaye ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Smart Adeyemi wanda ya samu sama da ƙuri’a 73,000.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan