Jirwaye: Ina Rayuwar Almajirai Ta Dosa A Ƙasar Hausa? (I)

228

Kowacce Al’umma tana sane da cewa, akwai babban hakki akan ta na kula da yara wanda, Al’ada (Culture), da al’umma (Society), ta dora masu, wanda in har akabar wannan hakkin ya sauka ko ba a kula dashi ba, to lallai an dauki hanyar tarwatsa tsarin zamantakewar yariwar dan adam gaba daya. Masana halayyar jama’a (Sociology), suna ganin cewa al’umma tana samun koma bayane ta barin kowa yayi rayiwarsa shi kadai. Wanda a turance ake kira da Individualism life, wannan rayiwa da ake bata da wani tasiri sai na koma baya.

BARA
Da yawa ana kai yara bara da sunan karatun Al-Qur’ani Mai Girma ta fuska me kyau, amma kuma ta daya fuskar bahaka abin yakeba; da yawa iyaye suna kai yaransu bara dan gudun daukar nauyinsu. Ina nufin gudun wahalarsu bayan kowa yana sane da cewa duk wanda ya haifi yara wajibi ne ya kula da tarbiyarsu, iliminsu, lafiyarsu da wajan kwanansu. Lokacin baya Malamai suna da Gona da suke saka almajiran su noma wadda suke samin abinda zasu ciyar dasu lokacin komai yana zaune lafia; ina ga yaran da suke gaban iyayen suma da yawa basa samun abinda zasu kai bakinsu balle a tuna da almajirai.

Almajirai

Tambaya ta anan shine Wanda bai sami abinda zai kai bakinsa ba a wuni kuma karatu aka turashi kanajin kuwa karatun zai samu, ko kuma nace da wanne zaiji karatun ko abinci. Mutumin da bai sami abinda zai sa abakinsa ba kaga baza kayi masa maganar zuwa asibiti ba a lokacin da bashi da lafia, yana da gatan gaske ne a wajan Malaminsa za a jika masa wani abu a bashi ya sha ko kuma a yimasa rubutu a bashi ya sha wanda ba haka ya dace dashi ba, Ni a iya tunanina da sanina wanda bashi da lafia asibiti ya kamata yaje yaga likita kaga kenan almajiri bashi da wannan gatan.

Lokaci da yawa zaka ga almajirai suna yawo a kan hanya sun fita daga cikin hayyacin su domin neman abinci, babu maganar karatu sai neman abinda zasu kai bakinsu.

To daga lokacin zasu shiga cikin wani hali mai wahala duk wanda ya basu abinci indai sun koshi zasu bishi koda kuwa mutumi nan ba mutumin Kirki bane. Duk wanda zaiyi karatun Al-Qurani yana bukatar kulawa daga wajan iyayensa kulawa da abincinsa, lafiyarsa kaya masu kyau saboda Qur’ani Maganar Allah ce kaga kenan ba abin wasa bane, babban bakin cikin da yake damuna zakaga Uba ya kawo dansa Bara tun yana dan shekara 6 yabar gaban iyayensa da sunan Bara, Mamanshi tana kuka bataso saboda rabuwa ba dadi amma kaga Uba ya dage sai ya kai shi, saboda gudun wahalar yaron bayan kai ne ka haifishi kuma kake gudun wahalarshi. Subahanallah wannan Uba kasan irin damuwar da Mamansa take shiga

Akwai ranar da zaku tsaya a gaban Allah tsakanin Yaro da Babansa a gaban Allah kayi bayani yadda ka rike amana, ranar kowa ta kansa yake babu wanda zai cece wani sai abinda Kazo dashi gaban Allah, ina kuma ga mutanan da suke tura yaran su bara da sunan karatu daga baya suzo su shiga sharafinsu, kuma Malamai suna zaune yarane zasuje suyi bara akawo wa Malam abincin da zai ciyar da gidansa kuma Malaman suna da salo me tarin yawa wajan tura yaran bara akwai Malaman da suke rubutu a hannun yaro wai agane ya ci abinci ko bai ciba dan, karyazo yayiwa Malam karya. Wanda suke rayiwa cikin birni kenan wanda suke rayiwa cikin Kauye kuma dama basu da aiki sai yiwa Malam noma, Yaro bashi da lokacin kansa ko na karatun sa.

A karshe a zo ayi biyu babu, ba karatu ga cutarwa. Almajiran dasu cikin Birni sune Wanda suke shiga sharafinsu na neman kudi ta kowacce hanya Dan ganin sun zama mutane amma marasa inganci a cikin Al’umma Iyaye sun taka rawa wajan lalata rayiwar Yaransu. Akwai lokacin da akai fira da wani Yaro Wanda aka kawosu Bara Garin Kano, abin takaici an turosu ne saboda.

Almajirai

Babansu yana san dakin da suke kwana zai kara aure. Wannan ba karamin abin ta kaici bane. Aure baya wajaba akan Wanda bashi da hali amma kulawa da Yara wajibi ne, in kuna haifar yaran da bazaku iya kulawa dasu bane to ku haifi iya wanda zaku iya daukar nauyinsu mana; saboda da kubuta daga wajan Allah tunda dai naji Malamai suna cewa Allah baya dorawa bawa abinda bazai iyaba sai dai bawa ya dorawa kansa abinda yafi karfinsa.

To mu dai na dorawa kanmu abinda yafi karfinmu mana. Saboda babu Wanda suke Haifa Yara suke ban zatar dasu sai mu Hausawa; sai kaga mutun daya albashin sa be wuce 20,000 amma matansa uku yana harin aurar ta hudu kuma bashi da wani tsari me kyau kan yaransa sai dai ya turasu Bara, Allah ya kyauta amin.

Shawara ga Malaman makarantar Bara lokaci yayi da kuma zaku dai na wahala akan yaran wasu. Kuma kuna da yarannan kuma kun haifa nauyinsu yana wuyanku kuma an zaunar daku an hanaku zuwa nema, me zai hana kuyi tsari kamar yadda makarantun kwana suke na Boko duk wanda zai kawo Dansa Bara yazo da kayan abincin sa na wata da kudin magani da sauran kayansa na bukata na rayiwa ace Yara sun dai na fita Bara.

Kuma duk bayan wata uku Uba yazo wajan dan sa, ya biya masa kudin makaranta duk bayan wata uku in mutun ya kasa yiwa yaransa haka sai a mai dashi garinsu. Kaga kenan babu Kare bin damo, saboda duk wanda zaiyi karatu yana bukatar kulawa in kuwa ba haka ba zakuci gaba da tara mutanan da basu da gobe me kyau.

Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com
08037340560

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan