Home / Siyasa / ‘Yan Najeriya na dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasa
Masu kaɗa ƙuri'a a kan layin zaɓe

‘Yan Najeriya na dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasa

‘Yan Najeriya na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, 2019 a dukkan fadin kasar.

‘Yanan takarar shugaban kasa sama 70 ne daga jam’iyyu daban-daban da suka shiga takarar ta shugabancin Najeriya.

Amma takarar ta fi zafi ne tsakanin shugaba mai ci, dan takarar jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Kawo yanzu dai jihar Ekiti ta gama tattara sakamakon zaben na shugaban kasa, kuma ana sa ran Baturen Zaben jihar zai gabatar da sakamakon a gaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasar, INEC a Abuja.

Hukumar ta ce a yau Litinin da misalin karfe 11 na safe za ta fara sanar da sakamakon zaben shugaban kasar.

A bisa doka dai, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi kadai yake da hurumin bayyana wanda ya lashe zaben.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Ni da Obasanjo mu ka kuɓutar da ɗaliban babbar kwalejin gandun daji ta Afaka – Sheikh Gumi

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana rawar da shi da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *