Ba dan takarar shugaban kasa da zai samu kuri’a sama da 55%- YIAGA AFRICA

117
YIAGA AFRICA

Wata kungiya mai suna YIAGA AFRICA ta ce babu dan takarar shugaban kasa a zaben da aka yi a kasar nan ranar Asabar da zai samu kuri’u sama da kaso 55%.

Kungiyar ta fadi hakan ne lokacin wani jawabi da ta yi kan yawan jama’an da suka fito kada kuri’a da kuma sakamakon zabe ta bakin Shugaba da Sakataren Kungiyar, Dakta Hussain Abdu da Samson Itodo.

Kungiyar ta tura wakilai masu sa ido a harkar zabe guda 3,906 da kuma wasu 3,030 a mazabu 1,515 wanda suka kawo rahotanni da suka nuna cewa babu dantakarar da zai samu sama da kaso 55% na dukkanin kuri’un da aka kada.

Kungiyar ta yi hakan ne domin taimakawa wajen samar da sahihan bayanai akan zabe ga ‘yan kasa, ‘yan takara da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC da kungiyoyjn sa kai.

Daga karshe, Kungiyar ta ce ta kammala karbar dukkanin rahotannin da tuke bukata kuma za ta gani ko sakamakon da Hukumar INEC za ta fitar zai yi daidai da bayanai da ta samu daga mazabu. Kungiyar ta ce Hukumar INEC ce kadai ke da ikon bayyana sakamakon zabe, don haka bayanai da kugiyar ta tanada za ta yi amfani da su ne don ganin cewa sakamakon yayi daidai da zabin jama’a.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan