‘Yan takarar Majalisun Tarayya na jam’iyyar PDP a jihar Borno sun yi watsi da sakamakon zaɓe

138
PDP

‘Yan takarar Majalisun Tarayya na jam’iyyar PDP a jihar Borno sun ki amincewa da sakamakon zaben da aka bayyana na jihar bisa zargin magudin zabe.

‘Yan takarar sun yi kira ga Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC Farfesa Mahmood Yakubu da Kwamishinan Hukumar Zabe na Jihar, Malam Mohammed Ibrahim da su soke zaben saboda rashin bin dokar da Hukumar INEC ta saka domin tabbatar da zabe cikin gaskiya.

Sun kara da cewa a wasu wuraren yawan kuri’un da ‘yan takarar APC suka samu ya fi yawan jama’ar dake da katin zabe kamar a mazabar Dikwa, Mafa da Konduga, dan takarar APC na da kuri’u 19,304, dan takarar PDP nada kuri’a 1,359 amma yawan mutane masu rigistar zabe 18,245 ne.

Daga karshe sun yi kira ga INEC da ta soke zaben ko kuma su shiga kotu domin kuwa ba su yarda da sahihancin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da aka yi ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan