Da ɗumi-ɗumi- Buhari ya ci zaɓe

189
Shugaba Muhammadu Buhari

A ranar Laraba ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019.

Shugaban Hukumar Zaben, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APCn ya samu kuri’a 15,191,487.

Babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu kuri’a 11,262,978 inda ya zo na biyu.

“Cewa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, sakamakon cika tanadin dokoki, da kuma samun mafi yawan kuri’u, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, ya kuma tabbata zaɓaɓɓe”, in ji Farfesa Yakubu.

Buhari ya kayar da Atiku ne da kuri’a sama da miliyan 3.
Tuni dai jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben tun kafin INEC ta sanar da shi a hukumance inda ta yi zargin cewa zaben cike yake da kurakurai a wasu wurare, kuma sakamakon bai yi daidai da wanda yake hannunta ba.

A ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, 2019 ne aka gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ‘yan Majalisun Tarayya a Najeriya bayan da Hukumar Zaben Kasar, INEC ta dage shi daga 16 ga watan Fabrairu sakamakon matsalolin rashin kai kayan aikin zabe a wasu sassan kasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan