Rikicin zaɓe a jihar Rivers: Rundunar Sojojin Kasa ta yi wawan kamu

148
Sojoji suna sintiri

Rundunar Sojojin Kasa ta Najeriya ta kama akalla mutane 35, bisa hannu wajen tada fitintinu a jihar Rivers a zaben ‘yan Majalisun Tarayya da na Shugaban Kasa da ya gudana ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu, 2019.

Babban Jami’i mai bada umarni na Shiyya ta 6 dake Fatakwal, Mejo Janar Jamil Sarham ne ya bayyana haka a lokacin da aka yi holin masu tada rikicin ranar Talata a hedkwatar Rundunar.

Wakilin Babban Jami’in, Kanar Aminu Iliasu ne ya bayyana haka a wajen holin mutanen ranar Talata a Fatakwal.

Ya ce wasu daga cikin mutanen sun sanya kaya irin na ma’aikatan Hukumar Zabe, kuma sun tada hargitsi a wajen zaben.

A tare da mutanen an samu faifan bidiyo inda aka gan su suna magana da gwamnan jihar, Nyesome Wike. Bayan an tuhume su, mutanen sun amsa cewa gwamnan ne ya sanya su wannan aikin.

Daga cikin mutanen da aka kama, akwai Kwamishinan Raya Birane na Jihar, Dakta Reason Onya, da dan majalisar dokoki mai wakiltar Ahoada ta Yamma , Nwanaka Okpokiri, da wani jami’in soja, Major Akpoge Peter Ubah, da jami’in dan sanda, DSP Oyoku Iffela da wasu ‘yan sanda Uku, da yan daba da ma’aikatan Hukumar Zabe.

Rundunar ta kama takardun zabe a hannun su kuma ta samu nasarar cafke mutanen bayan samun hadin kai daga sauran jam’an tsaro dake jihar.
Tuni an mika su zuwa hannun wakilin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar kuma Mataimakin Kwamishina mai kula da Sashin Binciken Manyan Laifuka, Ahmad Kontagora.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan