Wata Ƙungiyar Sa Ido Ta Bayyana Sakamakon Bincikenta Game Da Matsalolin Da Suka Dabaibaye Zaɓukan Najeriya

176
A'isha Bagudu da muƙarrabanta

Wata Kungiyar Sa Ido mai suna Election Observation Platform, EOP wadda Transition Monitoring Group TMG da Human and Environmental Development Agenda HEDA ke daukar nauyi ta bayyana sakamakon binciken da ta gudanar akan zaben Shugaban Kasa da na ‘yan Majalisu da aka gudanar a karshen mako.

A wata sanarwa da ta aika wa jaridar Sahara Reporters, Kungiyar ta zayyana cewa sayan kuri’u da dangwale ba bisa ka’ida ba na daga cikin abubuwan suka kawo tsaiko ga zaben.

A cewar Kungiyar, a wasu wuraren kuma matsalar satar akwati ce ta hana gudanar da zabe.

Kungiyar ta ci gaba da cewa jihohin da suka fuskanci wadannan matsalolin su ne Kano, Legas, Sokoto, Kogi, Abeokuta, Rivers da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Kungiyar ta ce, an fuskacin irin matsalolin da aka saba samu a lokutan zabe, kamar rashin kawo kayan aikin zabe akan lokaci wanda yakan janyo rashin gama zabe da bayyana kuri’u akan lokaci, zuwan ‘yan daba mazabu tare da tada hargitsi da hana gudanar da zabe, da kuma masu zuwa sanye da kayan ma’aikatan zabe ko na hukumomi ko na wakilan jam’iyya don wata manufa.

A wasu mazabu kuma a cewar Kungiyar an samu matsalolin tantance masu zabe, da kuma samun masu kada kuri’a fiye da daya, da kananan yara masu zabe da kona kayan aikin zabe.

A karshe, Kungiyar ta ce wadannan miyangun ayyuka sun yi karanci ba kamar a baya ba, kuma a wannan karo an samu ci gaba ba kamar a baya ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan