Bayanan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta fitar na baya-bayan nan sun nuna cewa 35 cikin dari ne kadai na wadanda suka yi rijista suka kada kuri’a a zaben Shugaban Kasa da na ‘yan Majalisun Tarayya da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.
Kason yana wakiltar mutane 28,614,190 da suka kada kuri’unsu a lokacin zabukan, wanda shi kuma yake wakiltar kaso 0.19 cikin dari na yawan mutanen da aka tantance wadanda suka kai jimillar kaso 35.66 cikin dari wato 29, 364,209 na wadanda suka yi rijista gaba daya.
Haka kuma bayanan sun nuna cewa kaso 33.18 cikin dari na sahihan kuri’u wato 27,324,583 daga jimillar mutane 82,344,107 da suka yi rijista su suka yanke hukuncin karshe.
Bayanan sun kuma nuna cewa jihar Kano ita ce jihar da aka fi kada kuri’a inda mutane 1,964,751 suka kada kuri’a, aka kuma samu sahihan kuri’u 1,891,134.
Jihar Jigawa kuma ita ce jihar da mutane suka fi fitowa zabe inda aka samu kaso 55.67 cikin dari daga cikin 1,171,801 na mutanen jihar da suke da rijista.
Jihar Katsina ita ce ta biyu da kaso 48.45 cikin dari, sai jihar Sokoto mai kaso 46 cikin dari na masu kada kuri’a sahihai.
Jihar Legas na sahun gaba a cikin jihohin da aka samu karancin fitowar masu zabe inda kaso 17.25 cikin dari ne kawai suka fito, sai jihar Abia mai kaso 18 cikin dari, sai jihar Rivers mai kaso 19.97 cikin dari.