Galadima ya taya Buhari murnar lashe zaɓe

182

Shugaban Jam’iyyar ACPN na Kasa, Alhaji Ganiyu Galadima ya taya Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC murna bisa nasarar lashe zaben Shugaban Kasa da ya yi.
Alhaji Galadima ya bayyana nasarar Shugaba Buhari a matsayin “abinda ya kamata sosai”.

Amma ya yi kira a gare shi da ya kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa manema labarai jiya a Abuja.

Ya yi kira ga Atiku da ya karbi faduwa ko kuma ya shigar da korafe-korafensa ta hanyoyin da suka dace ba tare da barin korafe-korafen su zama barazanar tsaro ga kasar nan ba.

“Nasarar Shugaba Muhammadu Buhari abu ne da ya kamata sosai duba da farin jininsa, karbuwarsa a dukkan fadin kasar nan da kuma kokarinsa a shekaru uku da rabi da suka gabata.
“Mu a matsayin jam’iyya tuni muka bayyana goyon bayanmu gare shi tun kafin zabe, kuma mun gode wa Allah cewa goyon bayan namu bai tafi a banza ba.

“Saboda haka, muna kiran Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da ya kalli nasarar Buhari a matsayin abinda mafi rinjayen ‘yan Najeriya suke so. Mutane sun yi magana. Muna sa ran a matsayinsa na mai son dimokuradiyya ya karbi faduwa ya ci gaba, ya sa a zuciya cewa Allah ne yake bada mulki”, in ji Alhaji Galadima.

“Mun kuma yi imani cewa Alhaji Abubakar da jamiyyarsa suna da damar kalubalantar sakamakon, amma muna bada shawara cewa ya kamata a yi hakan cikin lumana ba tare da jefa tsaron Najeriya da ‘yan Najeriya cikin hadari ba”, a cewar Alhaji Galadima.

“ACPN na bukatar Shugaba Buhari ya yi dukkan mai yiwuwa wajen hada kan kasar nan idan zai yiwu ta hanyar kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa wadda za ta kunshi dukkan masu ruwa da tsaki wadanda suke da abinda za su iya ba kasar nan”, a kalaman Alhaji Galadima.

Daga karshe jam’iyyar ta ACPN ta kuma yi kira ga Shugaba Buhari da ya kara kokari wajen kyautata harkar tsaro a kasar nan, ba kawai a yankin Arewa Maso Gabas ba, har ma ga dukkan sauran yankuna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan