Gidauniyar A’isha Bagudu ta tallafa wa marasa ƙarfi

246
A'isha Bagudu na miƙa kayan tallafi ga marasa ƙarfi

Gidauniyar A’isha Bagud mai dakin Gwamnan Jihar Kebbi, mai suna MALLPAI Foundation ta bayar da taimako akan harkar lafiya da ilimi kyauta ga rugagen Fulani guda 1000 tun daga kafa ta.

Jagoran Kungiyar, Malam Nurudeen Nasarawa ne ya bayyana haka a lokacin da Kungiyar ta cika shekaru 10 da kafuwa.
An kafa kungiyar ne a shekarar 2009.

Ya kara da cewa, Kungiyar an kafa ta ne da niyyar taimakawa marasa galihu da kawo ci gaban jama’a domin kyautata rayuwa.

A cewar Malam Nurudeen, daga shekarar 2015 zuwa 2017, Kungiyar ta koyar da dalibai 8000 sana’o’i da suka hadar da dinki, da aikin sa fanfo, gyaran jiki, aikin wutar lantarki, aikin kafinta, gyaran jiki, da saka tauraron dan Adam da aikin walda.

Bayan haka, Kungiyar ta samar wa almajirai 1000 guraben karatu a makarantun yaki da jahilci.
Ta biya musu kudin jarabawar WAEC da NECO kuma mafi yawan su, sun samu guraben karatu a jami’o’i da Kwalejojin Ilimi.

Daga karshe, Malam Nurudeen ya ce Kungiyar ta maida hankali wajen ganin matasa sun koyi sana’a kuma sun zama masu dogaro da kansu ta hanyar aiki da abin da aka koya musu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan