Wani jigo a jam’iyyar APC ya bayyana kutungwilar da PDP ke son shiryawa a Majalisar Dokoki

230
Yekini Nabena

Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na kasa, Yekeni Nabena ya yi zargin cewa jam’iyyar PDP tana shirin kwace shugabancin Majalisar Dokoki mai zuwa, inda ya yi kira ga jam’iyyar APC da kada ta kara maimaita kuskuren da ta yi a 2015.

Mista Naben ya ce don a guje wa rikicin siyasar da ya biyo bayan zaben shugabancin Majalisar Dokoki ta Kasa, ya zama dole shugabancin jam’iyyar ya fito da wani tsarin karba-karbr cikin gida na adalci da zai hada kowa da kowa domin ba masu ruwa da tsakin APCn damar samar da shugabannin da da take so a Majalisar Dattawa da ta Wakilai mai zuwa.

Da yake jawabi ga manema labarai ranar Asabar a Abuja, Mista Nabena ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya taka muhimmiyar rawa a tsarin zaben shugabancin cikin gida na APCn.

“Jam’iyyar PDP ta fadi zaben Shugaban Kasa, yanzu kuma sun dauko shirinsu na ‘B’ daga Taron Tattaunawarsu na Dubai don kwace shugabancin Majalisar Dokoki mai zuwa su maimaita mummunan juyin mulkin da suka yi a Majalisar da ta gabata.

“Dole jamiyyar APC ta kare maimaituwar yanayin da duk da irin rinjayen da muke da shi a Majalisar Dattawa da ta Dokoki taa 8, ‘yan ta bare da abokan hamayyarsu na PDP suka kwace shugabancin Majalisar Dokoki”, in ji Mista Nabena.

Mista Nabena ya ce ‘yan Najeriya za su iya tuna yadda Majalisar Dokoki mai barin gado ta 8 karkashin jagorancin Bukola Saraki ta dinga yi wa gwamnati mai ci zagon kasa.
Ya kara da cewa ba don jajircewar Shugaba Muhammadu Buhari ba da ba a samu nasarorin da aka samu ba kawo yanzu.

Ya ci gaba da cewa Majalisar Dokoki wani sashi ne na gwamnati mai matukar muhimmanci wanda za a iya amfani da shi don cimma Bukatar Canji da ake nema.

“Banda kasancewarsa Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari uba ne da ake girmama shi a tsakanin ‘yan jam’iyya da magoya baya. Shigarsa kai-tsaye da bayyana ra’ayinsa zai zama yana da muhimmanci sosai idan jamiyyar ta fara yunkurin karba-karba a shugabancin Majalisar Dokokin”, in ji Mista Nabena.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan