Jam’iyyar PDP a jihar Kano ta rasa wasu jigajiganta

179
PDP

Jam’iyyar PDP a jihar Kano na fuskantar rasa jagororinta inda tsagin da Mas’ud El-Jibrin Doguwa ke yi wa jagoranci suka bar jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC.

Sakataren Yada Labarai na tsagin, Musa Danbirni ya tabbatar da ficewar tasu ga jaridar Daily Nigerian, yana mai cewa za su yi wa manema labarai jawabi ranar Litinin domin su bayyana dalilansu na barin jam’iyyar ta PDP.

An gano cewa shugabanni 12 daga cikin 14 tare da magoya bayansu ne suka bi sahun Mista Doguwa inda suka fice daga jam’iyyar ranar Lahadi.

A ranar Asabar ma, wasu manya-manyan jagororin jam’iyyar da suka hada da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa, Imam Buhari; tsohon dan Majalisar Wakilai, Ahmed Salik; tsohon Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa, Surajo Marshall; wani dan siyasa daga tushe, Yahaya Bagobiri da sauransu sun bayyana shirinsu na goyon bayan takarar Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar Litinin din nan wata Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Kano ta soke zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP Reshen Jihar Kano ta ce ta yi, inda ta fitar da Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takararta na gwamna.
Kotun ta bukaci jam’iyyar PDP a Kano da ta sake gudanar da zaben fitar da gwani nan da mako biyu

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan